An sauke firaministan Sri Lanka daga mukaminsa
October 27, 2018Talla
Tuni dai wannan canji ya fara haifar da yamutsi a siyasar kasar ta Sri Lanka sakamakon ikirarin da firaminista mai barin mulki ya yi na cewar shi ke da mafi rinjayen magoya baya a zauren majalisar dokokin kasar, don haka ba zai sauka daga mukaminsa ba.
A nasa bangaren sabon firaministan ya shaida wa manema labarai cewar ya shirya tsaf don fara gudanar da aiki tare da shugaban kasa Maithripala Sirisena.
Shi dai Shugaba Sirisena wanda ya dauki tsawon shekaru tara yana mulki bayan yakin basasar da ya faru a kasar, ana zarginsa da cin hanci da karbar rashawa da kuma cin zarafin 'yan jarida da gana musu azaba.