1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Siriya da Mali sun kankane taron ƙungiyar OIC na bana

Usman ShehuFebruary 6, 2013

Shugabannin ƙungiyar ƙasashen Musulmai ta duniya sun mai da hankali kan rikin Mali da Siriya a taronsu da aka fara a birnin Alƙahira

Egyptian President Mohamed Mursi (first row, 12th L) stands with other leaders of Islamic nations for a group photo before the opening of the Organisation of Islamic Cooperation (OIC) summit in Cairo February 6, 2013. Leaders of Islamic nations called for a negotiated end to Syria's civil war at a summit in Cairo that began on Wednesday, thrusting Egypt's new Islamist president to centre stage amid political and economic turbulence at home. REUTERS/Egyptian Presidency/Handout (EGYPT - Tags: POLITICS) ATTENTION EDITORS - THIS IMAGE WAS PROVIDED BY A THIRD PARTY. FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. THIS PICTURE IS DISTRIBUTED EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
Shugabannin kasashen kungiyar OIC a AlkahiraHoto: Reuters

An buɗe taron ƙungiyar ƙasashen Musulmai ta duniya wato OIC, a birnin Alƙahira. Babban jadawalin taron zai fi mai da hankalini kan ƙasashen Siriya da Mali, waɗanda yanzu haka ke fama da tashin hakanli. Taron ya samu halartan shugabannin ƙasashe 26 daga cikin ƙasashe 57 mambobin ƙungiyar. cikin shugabannin da suke halarta harda na Jamhuriyar Islama ta Iran, wato Mahmud Ahmadinejad, dakuma shugaban ƙasar Turkiya. Da yake jawabin buɗe taron shugaban ƙasar Sinigal Macky Sall, ya buƙaci mahalarta taron da su tallafawa ƙasar Mali ta samu yancin ta, bayan barazanar yan ta'adda waɗanda suka addabi al'ummar arewacin Mali. Shugaban ƙassar Masar Muhammed Mursi, shine zai karɓi shugabancin ƙungiyar ta OIC daga hannun Sinigal.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mohammed Nasir Awal

AFP