1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Siriya na cigaba da daukar hankalin al'ummar kasa da kasa

January 31, 2012

Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya yi alkawarin gudanar da wata zama ta musamman domin tattauna hanyoyin shawo kan rikicin Siriya

Abdul-Ilah al-Khatib, left, United Nations Special Envoy to Libya, briefs members of the Security Council on the situation in Libya at U.N. Headquarters, Monday, April 4, 2011. (AP Photo/David Karp)
Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin DuniyaHoto: AP

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Mrs Hillary Clinton ta yi Allah wadai da ta'azarar da rikicin Siriya ke yi, kuma ta yi kira ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya, da ya daidaita rikicin. Dole ne hukumar kolin ta yanke hukuncin da zai taimakawa fararen hulan kasar a cewar Mrs Clinton.

Gwamnati a Damaskus ta sake tsaurara matakin amfani da jami'an tsaro a duk fadin kasar. A 'yan kwanakin da suka gabata kawai, kimanin fararen hula 100 suka hallaka.

Haka nan kuma, taron kolin kungiyar Tarayyar Turai da ya gudana a Brussels, shima ya yi kira ga Kwamitin Sulhun da ya yi iya kokarinsa wajen kawo karshen rikicin. Kwamitin zai gudanar da wani zama na musamman a wannan talatar a birnin New York, inda babban sakataren Majalisar da wakilan kungiyar hadin kan larabawan zasu tattauna irin ci-gaba ko kuma ma akasi da ake samu.

"A jawabin da ta yi da manema labarai, ita ma jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Susan Rice

ta yi godo ga kwamitin sulhun, da ya goyi bayan shirin kungiyar Larabawan"

A ra'ayinmu mun san cewa yana da mahimmanci kwamitin ya tashi tsaye ya goyi bayan wannan shirin wanda duk kasashen da ke makotaka da mu suka zo suka roke mu da mu goyi bayan shi.

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Yahouza Sadissou Madobi