1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Siriya ya fara lafawa

April 22, 2012

Masu sanya ido na Majalisar Ɗinkin Duniya sun yi rangadin birnin Homs na Siriya dake fama da rikici a baya.

REFILE - CORRECTING SPELLING COLONEL'S NAME Colonel Ahmed Himmiche (C), a member of a U.N. monitors team, speaks to the media at a hotel in Damascus April 16,2012. A United Nations advance observers' team arrived in the Syrian capital Damascus late Sunday to monitor the fragile cease-fire brokered by international envoy Kofi Annan, causing discussion from all circles in Syria. REUTERS/Khaled al- Hariri (SYRIA - Tags: CIVIL UNREST MILITARY POLITICS)
Tawagar sanya ido akan tsagaita wuta a SiriyaHoto: Reuters

Masu sanya ido na Majalisar Ɗinkin Duniya biyar ne suka yi shawagi da ƙafufun su, kuma ba tare da wata matsala ba a sassa daban daban na birnin Homs - mai fama da tashe-tashen hankula a ƙasar Siriya. A lokacin rangadin da suka yi a wannan Asabar, titunan birnin na nan sit bayan makonnin da aka yi ana luguden wuta, yayin da kuma mazauna birnin ke yin ƙira ga samun taimakon dakarun ƙetare wajen kawar da mulkin shugaba Bashar al-Assad. Masu sanya idon dai na cikin tawagar farko ta mutane takwas da suka fara isa Siriya domin sanya ido akan yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakanin gwamnati da kuma 'yan adawar ƙasar.

Sai dai kuma masu fafutukar sun ruwaito cewar an sami 'yan harbe-harbe nan da can, amma ba'a sami luguden wutar da aka saba yi a baya ba, kana dakaru sun janye manyan tankunan yaƙi da kuma makamai daga birnin. A ƙarƙashin wata ƙwarya-ƙwaryar yarjejeniyar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta cimma tare da Siriya dai, masu sanya idon za su iya tafiya da ƙafafunsu da kuma tuƙa motocinsu ba tare da wata tsangwama ba. Sai dai kuma Siriya ta ƙi amincewa da buƙatar Majalisar Ɗinkin Duniya na cewar tawagar sanya idon ta yi anfani da jiragenta wajen yin shawagin.

A halin da ake ciki kuma Rasha ta buƙaci Faransa da ƙawayen ta dasu nuna halin ya kamata domin kawo ƙarshen rikicin Siriya cikin lumana, kamar yanda jakadan Rasha a Majalsar Witali Tschurkin ya faɗi:

"Ya ce gungun ƙasar Faransa da ƙawayen ta dake muradin cimma wata buƙatar su, kamata yayi su mutunta ƙudirin kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya akan Siriya, amma ba su rinƙa neman gurguntashi ba ta hanyar ɗaukar wasu matakai."

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Halima Balaraba Abbas