Rikicin Siriya ya mamaye taron kolin Kungiyar G-8
June 17, 2013Matsayin kasar Rasha na taimaka wa Siriya ya dagula tattaunawar da ake yi tsakanin shugabannin G-8 a daidai lokacin da kungiyar ta fara taron kolinta na shekara-shekara a Ireland ta Arewa. Kin gwamnatin Mosko na goya wa kasashen yamma baya a yakin da aka kwashe sama da shekaru biyu ana yi a Siriya ya mamaye sanarwar da aka bayar a zauren taron cewa Amirka da Tarayyar Turai sun kaddamar da wani yankin ciniki maras shinge da zai hade manyan yankunan duniya masu karfin tattalin arziki. Yayin da Amirka da Birataniya da kuma Faransa ke shirin tura wa 'yan tawayen Siriya da makamai, shugaban Rasha Vladimir Putin ya sake kare matakin tura makamai da kasarsa ke ci gaba da yi ga gwamnatin Bashar Al-Assad, domin a cewarsa ita ce halastacciyar gwamnatin kasar. Firaministan Birtaniya David Cameron ya ce har yanzu akwai sabani tsakani inda ya ce:
"Kun dai ga babban bambamcin dake tsakaninmu game da abubuwan dake faruwa a Siriya da kuma wanda ya kamata a dora wa laifi. Amma mun samu matsaya daya game da aukuwar wani bala'i ga dan Adam. Dukkanmu mun ga hadarin rashin zaman lafiya da tsattsauran ra'ayi. Dukkanmu muna goyon bayan taron samar da zaman lafiya a Siriya."
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar