1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasa a kasar Masar

June 28, 2013

Dubban Misirawa masoya da makiyan Mohammed Mursi suka fito domin halartar gangami

Opponents of Egypt's Islamist President Mohammed Morsi wave national flagsin Tahrir Square in Cairo, Egypt, Friday, June 28, 2013. Elsewhere, thousands of supporters of Egypt's embattled president are rallying in the nation's capital in a show of support ahead of what are expected to be massive opposition-led protests on June 30 to demand Mohammed Morsi's ouster. (AP Photo/ Amr Nabil) pixel
Hoto: picture alliance/AP Photo

A wannan Lahadin ne dai bangarorin biyu suka shirya gagarumar zanga-zanga ta neman shugaba Mohammed Mursi da ya yi marabus. Wannan babban gangami da 'yan adawar suka kira, ya zo daidai da bukukuwan cika shekara guda da shugaban ya yi a kan karagar mulki.

Mohammed, mai shekaru goma dake zaune a wani wurin sayar da shayi yana yin taɗi da abokansa ya zaɓu wannan rana ta zo domin nuna fushinsa ga gwamnatin 'yan uwa Musulmi ta Mohammed Mursi wacce tun zuwanta kan gadon mulki abubuwa suka taɓarɓare wa al'ummar domin a cewarsa, shi a kowace rana ko Euro ɗaya ba ya samu, misali a duk bige-bigen da yake domin ciyar da iyali:

"Jama'a na cikin matsi gwamma jiya da yau sau dubu, ya ce Mubarak da sauran ministocinsa sun fi wannan gwamnat nesa ba kusa ba."

Mohammed MursiHoto: Imago

Al'umma na zargin gwamnati da rashin cika alƙawura

Gwamnatin dai ta Mursi ta gaza cika alƙawura da dama, yayin da ake da matsalar cire wutar lantarki da ƙarancin man fetur da dai sauran ababen na rayuwa da suka yi wuya. Abin da ya sa kenan ƙungiyoyin 'yan adawar da na farar hula za su gudanar da zanga-zanga ta kyamar gwamnatin Mursi a fadar shugaban kasar. Jan Dagos na daga cikin wadanda suka tsara wannan gangamin.

"Jama'armu da dama daga cikin waɗanda suka saka hannu a kan wannan takardar ta amincewa da marabus na shugaba Mursi an kai masu hare-hare, mata hade da maza ba bambanci."

Yunƙurin ganin Mursi ya yi murabus

Hoto: Str/AFP/Getty Images

Ƙungiyoyin dai sun ce sama da mutane miliyan goma ne suka saka hannu a kan takardar ta neman gwamnatin ta yi marabus. Tun farko dai rundunar sojojin kasar ta ce ba za ta sake saka ido ba ta yi kallon yamutsen da jama'ar ƙasar ke yi abin da kuma Mohammed ya ce su suna ma fatan sojoji su ƙwace mulki.

"Ina son soji su yi wani yunƙuri su kawo gyara ga halin da ake ciki, su kama dukannin ɓarayin ƙasa da wadanda suka aikata kisan kai da makami."

Yanzu haka dai jama'a da dama a kasar ta Misira na cikin fargaba saboda ba wanda ya san abin da zai faru a ranar Lahadin kuma tuni dai jama'ar ƙasar suka fara sayen abinci da man fetir suna ɓoyewa, tare kuma da cire kuɗaɗe a bankuna.

Mawallafi: Abdourahmane Hassane
Edita: Umaru Aliyu / USU