1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasa a Pakistan

January 19, 2012

Frime Ministan Pakistan ya karyata zargin kin bin umurnin kotu, bayan da ta bukace shi da ya bada izinin gudanar da sharia kan shugaban kasar Asif Ali Zardari, bisa zarginsa da almundahana

Pakistani Prime Minister Yousuf Raza Gilani gestures during an interview with The Associated Press at his residence in Lahore, Pakistan, Monday, Dec. 5, 2011. Gilani says his country wants to rebuild ties with the United States despite Islamabad's ongoing retaliation for deadly airstrikes on its troops by the U.S.-led coalition in Afghanistan. (Foto:Muhammed Muheisen/AP/dapd)
Firaministan Pakistan Yousuf Raza GilaniHoto: AP

Frime Ministan Pakistan Yusuf Raza Gilani ya bayyana a gaban kotun kolin kasar domin kare kansa daga zargin da aka yi masa na yi wa babban kotun kasar tsiwa. Inda ya bayyanawa kotun cewa shugaban kasa yana da rigar kariya ya kuma kare kansa daga zargin da ake masa na yin kunen uwan shegu ga umurnin kotun da ya bukace sa da ya nemi gwamnatin Swiss ta gudanar da sharia kan karar da aka gabatar mata. Kotun ta aikawa Gilani takardar sammaci ne bayan da ya ki yayi biyayya da umurnin da ya bukace shi ya rubuta wasika ga hukumomin swiss da su gudanar da shari'a kan zargin da akewa shugaban kasar wato Asif Ali Zardari wanda a yanzu haka yake shugabantar jamiyyyar Pakistan People's Party wacce ke mulki, na yunkurin mayar da kudin haram ya zama halak. Idan har Kotun ta same shi da laifin take umurninta Gilani ka iya rasa aikinsa. Wannan irin hukunci dai ka yi jefa Pakistan cikin wani hali na rikicin siyasa a irin wannan lokaci da kasar ke fama da matsaloli na karayar tattalin arziki da kuma yakin da take yi da ta'addanci. Kawo yanzu dai an dage shari'ar zuwa ranar daya ga watan Fabrairu mai zuwa.

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Umaru Aliyu