Shugaban Koriya ta Kudu na tsaka mai wuya
December 6, 2024Lamura suna kara sukurkucewa Shugaba Yoon Suk Yeol na kasar Koriya ta Kudu da ake ci gaba da samun bangarori masu goyon bayan matakin tsige shi daga madafun iko, bayan kafa dokar ta-baci na wani takaitaccen lokaci, inda yanzu haka shi kansa shugaban jam'iyyar PPP mai mulki yake goyon bayan matakin tsige shugaban kasar.
Karin Bayani: An shiga rudani bayan shugaban Koriya ta Kudu ya kafa dokar ta-baci
Gobe Asabar da yamma 'yan majalisa na bangare adawa za su dauki matakin jefa kuri'ar tsige shugaban na Koriya ta Kudu. Kuma saboda tsaron abin da ka iya faruwa 'yan majalisar za su ci gaba da kasancewa a zauren majalisar har zuwa lokacin kada kuri'ar, saboda inda suka fice daga zauren majalisar, Shugaba Yoon Suk Yeol ka iya daukan wasu matakan da za su iya rikita siyasar kasar.
Ana bukatar kaso biyu bisa uku na kuri'un 'yan majalisar domin tsige shugaban kasar. Ita dai majalisar dokokin Koriya ta Kudu tana da mambobi 300, inda 'yan adawa suke da kujeru 192 daga cikin adadin.