1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasar Gambiya na kara daukar zafi

Ramatu Garba Baba
September 24, 2020

Fatan samun sauyin gwamnati a Gambiya ya fuskanci tsaiko baya da majalisar dokoki ta yi fatali da sabuwar ayar dokar da aka gabatar mata don a takawa shugaba kasar birki a yunkurinsa na cigaba da kasancewa kan mulki

Gambia Präsident Adama Barrow kündigt Wahrheitskommission an
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Al'ummar kasar Gambiya da kuma masharhanta gami da kwararru kan dokokin kasar na cigaba da tofa albarkacin bakunansu kan kokarin shugaban kasar Adama Barrow na cigaba da kasancewa kan gadon mulki, duk kuwa da cewar wa'adin mulkinsa zai kare ne a cikin shekara mai kamawa. Guda daga cikin masu tsokaci kan wannan batu shi ne Dawda Jallow, alkalin alakalan kasar inda yake cewar ''mafita daya ita ce a koma a sake nazari a shata sabuwar doka da muke fatan ba za a iya fatali da ita ba.''

A daura da wadannan kalamai na Mr. Jallow, Sait Matty Jaw wanda malami ne a sashen nazarin siyasar duniya da ke a babbar jami'ar kasar ta Gambiya ya ce an rasa damar mai da kasar turbar mulkin dimokradiya, inda yake cewar ''na san ba yadda za a samar da irin wannan mulki na dimokradiya da tsohuwar ayar dokar kasar nan, Shugaba Barrow na da karfin iko don kuwa kundin tsarin mulkin kasar ne ya ba shi karfin ikon''

Shugaba Barrow da a wa'adin mulkinsa na farko ya yi farin jini a tsakanin matasa, a yanzu ya koma dattijon da matasan ke cewa ya ki mutunta alkawarinsa inda ya ke son cin albarkacin abin da dokar kasa ta fadi duk da alkawarin da ya daukar wa jama'ar na yin shekaru uku kacal.

Baya ga batu na kin mutunta alkawarin da ya dauka, 'yan kasar da dama a halin yanzu na nuna rashin jin dadinsu da irin salon mulkin Shugaba Barrow musamman ma idan ana magana ta tattalin arziki wanda ake cewar tagomashinsa na yin kasa, baya kuma ga matsala ta rashin aikin yi da matasa ke fama da shi.
 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani