Rikicin siyasar Jam'iyyar NNPP a Kano
October 15, 2024Bayyanar kungiyar Abba tsaya da kafar ka, da wasu mutane suka kirkiro tare da fara yada angizon ta a kafafen sada zumunta da gidajen radio shine ya zamo tushen rigima a cikin jamiyyar NNPP mai mulki a jihar Kano. Da fari dai an zargi sakataren gwamnatin jihar da zama madugu uban tafiyar kirkirar wannan kungiya sai dai a wani zaman sulhu da gwamnan jihar ya yi don dinke baraka a tsakanin 'yan jamiyyar, Dr Abdullahi Bappa Bichi sakataren gwamnatin jihar da ake ganin ya kulla shirin zaman doya da manja tsakanin sa da Madugun jamiyyar ya bayyana cewar ko kadan ba shi da hannu cikin kungiyar ta Abba tsaya da kafar ka.
To amma wani abu da ke kara nuna jikewar rikici a jamiyyar shine sanarwar da shugaban jamiyyar ta NNPP Hashimu Dungurawa ya bayar wacce ya bayyana dakatar da sakataren gwamnatin tare da kwamishinan sufuri Muhammad Digol, lamarin da ke kara nuna cewar har yanzu akwai sauran rina a kaba
A waje guda kuma an sami tsagewar jamiyyar ta NNPP zuwa gida 2 bayan da wani tsagi karkashin jagorancin Barrister Dalhatu Shehu Usman ya bayyana yana mai ikirarin cewar shine halastaccen shugaban jamiyyar mai mulki a jihar Kano.
Wani abu kuma shine yadda rikicin na jamiyyar NNPP ya zaman a hadin gambiza domin hatta ga shugaban kungiyar Abba tsaya da kafar ka dan jamiyyar adawa ta NNPP ne .
Wannan dai wata babbar guguwa ce da ta taso wa jamiyyar daga cikin gida kuma matukar ba an yi kokarin kashe ta, ta hanyar dabara ba za ta iya kassara jamiyyar gaba daya kamar yadda masana ke bayyanawa.