1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasar Libiya ya yi awon gaba da Firayi minista

October 7, 2012

Majalisar dokokin Libiya ta jefa Kuri'ar tunɓuke shugaban gwamnatin kasar Mustafa Abu Shagur daga bakin aiki.

Members of the Libyan military hold weapons and ammunition handed over to them by civilians in Tripoli's Martyrs' Square September 29, 2012. Hundreds of Libyans handed over weapons to the military in Tripoli and the eastern city of Benghazi as the authorities try to clean the streets from arms left over from last year's war. REUTERS/Ismail Zitouny (LIBYA - Tags: POLITICS MILITARY)
Hoto: Reuters

Majalisar dokokin Libiya ta kaɗa ƙuri'ar yanke ƙauna ga Firayi ministan ƙasar Mustafa Abu Shagur, bayan ta sake watsi da sunayen da ya gabatar mata na majalisar gudanarwa, da ta ƙunshi ministoci 10 a wannan Lahadi.

Wannan matakin, ya zo ne kwanaki huɗu bayan majalisar ta yi fatali da sunayen da aka gabatar a gabanta. Ranar Larabar da ta gabata, 'yan Libiya da suka harzuƙa sun kutsa cikin majalisar, bayan da majalisar ta yi watsi da sunayen ministoci 27 da Firayi ministan mai barin gado ya miƙa.

'Yan majalisa 125 su ka jefa kuri'ar yanke ƙauna, domin sauke Firayi ministan ƙasar ta Libiya Mustafa Abu shagur daga muƙaminsa, yayin da 44 su ka jefa kuri'ar ƙin amincewa. Wannan ya afku ne bayan cikar wa'adin kwanaki 25 da tsarin mulki ya nemi Firayi minista ya kafa gwamnati, kuma shi ne Firayi minista na farko da aka zaɓa tun bayan boren da ya hamɓarar da gwamnatin Marigayi Mu'ammar Gaddafi cikin shekarar da ta gabata ta 2011.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh