Rikicin siyasar Saliyo na kara dagulewa
March 23, 2015Jam'iyyun adawa a Saliyo sun ce sun fara tunanin kauracewa yin aiki da gwamnatin kasar saboda abinda suka kira rashin bin ka'ida kan sallamar mataimakin shugaban kasar Samuel Sam-Sumana daga bakin aiki da aka yi.
'Yan adawar har wa yau sun ce za su shige gaba wajen ganin an kaddamar da shirin tsige shugaban kasar Ernest Bai Koroma daga gadon mulki kana sun ce za su nemi kotun kolin kasar da ta duba batun sallamar da aka yi wa Mr. Sam-Sumana daga aiki a makon jiya.
A kwanakin da suka gabata ne dai jam'iyyar da ke mulkin kasar ta kori mataimakin shugaban kasar bisa zargin yi mata zagon kasa, kana shugaban kasar ya sanar da sallamarsa daga bakin aiki. Al'ummar kasar da kungiyoyi masu rajin kare dimokradiyya dai sun soki lamirin shugaban kasar kan wannan batu.