1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Rudanin siyasar Senegal

Rakia Arimi Robert Adé/SB
February 19, 2024

Sannu a hankali 'yan kasar Senegal sun fara samun 'yancin gudanar da zanga-zanga kwanaki kalilan bayan da kotun tsarin mulki ta yi watsi da kudiri dage zabe. Yayin da ake dakon sabon jadawalin zaben shugaban kasa.

Senegal Protest in Dakar
Hoto: John Wessels/AFP

Kimanin yan adawar siyasa 300 da aka kille a gidan yari ne aka yi wa sakin wucen gadi a cikin kwanaki 2 a kasar senegal. Yawancin su dai, an kama su ne a yayin zanga-zangar kin jinin gwamnati ko kuma bayan wallafe-wallafe a shafukan sada zumunta dona nuna adawa ga mulkin Shugaba Macky Sall. Nina Penda Faye, memba ga kungiyoyin farar fula na cewar sakin ganga ce mai baki biyu. saboda tun farko an taka doka. Bara Dieng, kafinta mai shekaru 39 da haihuwa ya kwashe watanni takwas a gidan yari, kafin a sake shi ne a makonnin da suka gabata. Amma ya ce zai nemi kotu ta bi masa kadi saboda ba a mutunta hakkinsa ba. Shi dai ya kasance mai goyon bayan jam'iyyar adawa ta Ousmane Sanko kuma har gida aka kama shi.

Karin Bayani: Senegal: Rikicin siyasa ya dauki sabon salo

Hoto: Maria Gerth-Niculescu

Wannan sakin fursunonin siyasa na faruwa ne a yayin da 'yan kasar Senegal da dama ke son ganin an gudanar da  zaben shugaban kasa. A halin yanzu ma dai, hadin gwiwar kungiyoyin da ke neman girka zaman lafiya ya ba da shawarar  gudanar da zaben shugaban kasa tsakanin ranar 3 zuwa 10 ga watan Maris na 2024. A nasu bangaren, yawancin 'yan siyasa na Senegal na kira da a gudanar da shi kafin ranar 2 ga watan Afrilu, ranar da wa'adin mulkin Shugaba Macky Sall zai kare, wanda a cewar Djibril Gningue kwararre kan harkokin zabe zai yi lokacin da hukunci da kotun tsarin mulki ta yanke. A yanzu haka dai, ana ci-gaba da ganawa tsakanin shugaba Macky Sall mai barin kujerar mulki da 'yan takarar zaben shugaban kasa 20 domin ganin an samu masalaha al'amuran siyasa da zamantakewa a tsakanin mutane.