1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasar Siriya ya ƙara ƙamari

October 25, 2011

Shugabanin adawar Siriya sun yi kira ga al´ummar ƙasa da ƙasashen duniya su taimaka domin kare rayukan fararen hula.

Hoto: dapd

Majalisar haɗin kan ƙasa ta Siriya wacce ta tara shugabanin adawa fiye da 140 ta yi kira ga alummar ƙasa da ƙasa da ta taimaka wajen kare fararen hular ƙasar. Kasancewar jami'an tsaro sun ƙara matsa ƙaimi wajen murƙushe masu zanga-zangar ƙasar. Tuni dai ƙasashen ƙetare su ka fara matsawa gwamnati a Damascus bayan da ƙungiyar kare haƙƙin bil Adama ta Amnesty International ta yi zargin cewa da hannun asibitocin gwamnatin ƙasar a azabtar da masu adawa waɗanda suka yi rauni.

Aƙalla mutane tara suka hallaka a tarzomar ta yau a ciki har da jami'an tsaro bakwai waɗanda suka mutu a lardin Idlib da ke arewa maso yammacin ƙasar. Rami Abdulrahman wani ɗan siriya da ke aiki da ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Human Rights Watch a London, ya faɗawa kamfanin dillancin labarun Jamus cewa, wasu masu ɗauke da makamai ne waɗanda ake kyautata zaton jami'an tsaron ƙasar da suka canza sheƙa ne suka kai harin. To sai dai wasu 'yan adawan da ke Siriya waɗanda ke tattaunawa da gwamnatin na Al-Assad sunce har yanzu suna da damar komawa teburin tattaunawar. Sun kuma yi kira ga sauran ƙasashen larabawa da su taimaka masu wajen shawo kan wannan rikicin.

Mawallafiya: Pinado Abdu

Edita: Yahouza Sadissou Madobi