1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Rikicin Somalia da karewar wa'adin dakarun kungiyar AU

Abdul-raheem Hassan M. Ahiwa
December 29, 2021

Somaliya na fuskantar sabon rikicin siyasa. Daga jan kafa kan zabuka da yakin neman zabe da ta'addanci da ke dagula lamura daidai lokacin da wa'adin dakarun AU ke cika.

Somalia Premierminister Mohamed Hussein Roble
Hoto: Feisal Omar/REUTERS

Majalisar Dinkin Duniya ta amince da sake fasalin rundunar AMISOM, yayin da Tarayyar Afirka ta fi son hada kai da Majalisar Dinkin Duniya. Gwamnatin Somaliya ta yi watsi da zabin bangarorin biyu. Tana son a karkatar da dukiyar kasa-da-kasa zuwa gina sojojinta na cikin gida. Wasu manyan masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa, sun ce ya kamata Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar AU su jira har sai kafuwar sabuwar gwamnati da aka zaba kafin ta fara neman ra'ayoyinta.

Sai dai galibin manyan abokan huldar kasa-da-kasa na Somaliya ba 'yan Afirka ba ne, don haka kokarinsu na samun hadin kai cikin sauki a karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya. Matt Bryden m,ai sharhi kan siyasa da tsaro a kasar, ya ce 'yan sandan Somaliya ba su zama na kowa ba, don haka ana bukatar dakarun AU don gudanar da sahihin zabe da mika mulki cikin lumana.

''Rundunar ‘yan sandan Tarayyar Somaliya ba ta tsaka-tsaki kuma ba za a iya dogaro da ita don kare tsarin zaben ba. Hakika, faifan bidiyo na baya-bayan nan na magudin zabe da aka yi a Mogadishu, ya nuna jami'an 'yan sanda a tsaye. Hadin gwiwar runduna, ciki har da 'yan sandan Jihohi membobi na Tarayya da na Majalisar Dinkin Duniya ko na AMISOM ne kawai za a iya la'akari da su a matsayin amintattau da za su yi wa kowa adalaci.''

Hoto: picture alliance/dpa

Yanzu haka dai kungiyoyin farar hula a Somaliya sun yi imanin cewa, nasara kalilan dakarun AU suka samu tun bayan zuwan su Somaliya a shekarar 2007, domin yakar kungiyoyin 'yan ta'adda, da kuma taimakawa wajen kare gwamnatin tarayyar da ke samun goyon bayan kasashen yamma. Ko a baya-bayan nan an samu labarin mutuwar mutane sakamakon barkewar fada tsakanin sojoji da ke gaba da juna a tashar jirgin ruwa da ke birnin Bosaso.