1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin SPLA da gwamnatin Sudan

Zainab MohammedNovember 19, 2007

Shugaban yankin kudancin Sudan Salva Kiir,ya zargi gwamnatin Khartum da shirin afkawa yankin da karfin soji.Bayan komawarsa gida domin fuskantar rikicin siyasa mafi daɗewa a Afrika da ƙasar sa ke fama dashi daga Amurka,Kiir ya fadawa Dubban gangamin waɗanda suka tarye shi cewar,bai komo gida domin ya shigar dasu faɗa ba,amma a shirye yake wajen ɗaukar matakai na kare kai.Wannan dai na mai zama sabon babi a sa in sa dake tsakanin jammiiyyarsa ta SPLM,da tsohuwar takwarar siyasar ta dake yankin arewaci.A watan daya gabata ne dai ministocin yankin kudancin Sudan ɗin suka fice daga gwamnatin shugaba Omar al-Bashir,adangane zarginsa da kin aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a shekara ta 2005,wanda ya kawo karshen yakin sama da shekaru 20 a wannan kasa.