Rikicin Sudan da Sudan ta Kudu
April 19, 2012Wannan kai ruwa ranar tsakanin ƙasashen biyu da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa ta sanya shugaban Sudan Omar Hassan al-Bashir cewar zai koyawa mahukuntan Sudan Ta Kudu hankali matsawar ba su janye dakarunsu daga Heglig ba wanda a cewarsa ya ke arewacin Kordofan saboda haka mallakin Sudan ne ba na Sudan Ta Kudu ba.
Shugaban Sudan Omar Hassan al-Bashir ya ce 'yan uwana lokaci ya yi da za mu fadawa juna gaskiya. Mun shirya mutuwa ko dai a Kahrtum ko kuma Juba. Jama'ar Sudan, musamman matasa mun daura ɗamarar yaƙi kuma da yaddar ubangiji za mu murƙushe waɗannan marasa gaskiya wato dakarun SPLA'.
To sai dai duk da waɗannan kalaman na shugaban Sudan, ita ƙasar Sudan Ta Kudun ta bayyana cewar ba ta shirin shiga yaƙi da Sudan ba kuma ba ta da niyyar haka kamar yadda ministan watsa labaran Sudan Ta Kudun Barnaba Marial Benjamin ya shaidawa manema labarai.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Zainab Mohammed Abubakar