Sudan: Rikicin Hausawa da yan kabilar Berti
July 20, 2022Talla
Mutanen da rikicin Hausawa da kabilar Berti ya halaka a Sudan sun kai 105. A ranar Asabar da ta gabata aka fara rikicin a yankin Sudan da ke makwabtaka da kasashen Habasha da Sudan ta Kudu. Lokaci zuwa lokaci dai rikicin kabilanci kan mallakar filaye irin wannan kan faru a kasar ta Sudan da ke a gabashin Afirka.