1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Rikicin Sudan ya kazance

Suleiman Babayo MAB
October 27, 2025

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan aikata ta'asa a garin da mayakan RSF na Sudan suka kwace daga dakarun gwamnati.

Mutanen da suka tagaiyara a garin El-Fasher na Sudan
Mutanen da suka tagaiyara a garin El-Fasher na SudanHoto: AFP/Getty Images

Hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi a wannan Litinin kan hali da ake ciki a garin El-Fasher da mayakan RSF da ke fafatawa da dakarun gwamnati suka bayyana kwacewa. Tun watan Mayu na shekarar da ta gabata ta 2024 ake kai ruwa rana tsakanin bangarorin domin kwace iko da garin na El-Fasher wanda ke zama gari mai tasiri a yammacin Darfur.

Yuwuwar aika ta'asa

Mutanen da suka tagaiyara a garin El-Fasher na SudanHoto: UNICEF/Xinhua/IMAGO

Shugabar hukumar kare hakkin dan Adam na majalisar Volker Turk ya fitar da wata sanarwar da ke nuni da yuwuwar samun aikata ta'asa daga bangaren mayakan da suka kwace iko da garin na El-Fasher.

Tun watan Afrilun shekara ta 2023 fada ya barke tsakanin sojojin gwamnatin Sudan da mayakan rundunar RSF.