1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sudan: Ana bukatar tallafin dala biliyan uku

Ramatu Garba Baba
May 17, 2023

Hukumar bayar da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA ta ce, tana bukatar akalla dala biliyan uku a gudanar da aikin agaji ga miliyoyin da rikicin Sudan ya daidaita.

Sudan na bukatar tallafin duniya
Sudan na bukatar tallafin duniyaHoto: JOK SOLOMUN/REUTERS

Majalisar Dinkin Duniyar ta yi kira ga manyan kasashen duniya, kan su taimaka wa wadanda rikici ya daidaita a Sudan da ma kasashe da ke kewaye da ita. Hukumar bayar da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA ta ce, tana bukatar akalla dala biliyan uku a gudanar da aikin agaji ga masu bukatar taimakon ya zuwa watan Oktoban bana.

Rabin al'ummar kasar Sudan miliyan arba'in da tara na dogaro da agajin Majalisar Dinkin Duniya a samar musu da abinci da ruwan sha da kuma wuraren zama na wucin gadi da sauran bukatun kiwon lafiya. Mutum sama da dari takwas aka tabbatar sun mutu baya ga wasu dubbai da suka ji rauni da kuma miliyoyin da suka tsere daga kasar.