1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici tsakanin Turai da Turkiyya kan 'yan gudun hijira

March 2, 2020

Ba zato ba tsammani sai ga shi an fada sabon rikicin 'yan gudun hijira. Turkyiya ta hankado 'yan gudun hijira zuwa Turai. Yanzu dole ne EU ta kula da 'yan gudun hijirar da kanta. 

Hoto: picture-alliance/dpa/A. Deeb

Shekaru hudu Tarayyar Turai ta bar Turkiya a matsayin shingen da ake kula da 'yan gudun hijira. Yanzu shugaban kasar ta Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya aiwatar da kalaman da ya sha yin barazana a akai. Turkiya ta kwaso 'masu neman mafakar siyasa da sauran 'yan gudun hijira ta sako su kan iyakar Girka da Bulgeriya. 


Yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Turai da Turkiyya wace aka baiwa Turkiyar kudi don ta tsugunar da 'yan gudun hijira yanzu shugaba Erdogan ya yi watsi da ita, ma'ana dai zai yi amfani da 'yan gudun huijira don biyan bukatun siyasarsa.

 

Sai dai ko wadanne manufofin siyasa Erdogan ke son cimma bisa wadannan matakan ba zata, kawo yanzu babu tabbas. Samun wata yarjejeniya fiye da wace aka kulla da shi a baya dai, da wuya hakan ya samu.


Gaskiya ne Turkiyya na dauke da 'yan gudun hijiran Siriya sama da miliyan uku. Kuma akwai alamar samun kwararar wasu 'yan gudu hijira daga Idlib inda yanzu ake yaki, wadanda za su nemi shiga Turkiyya. Wannan abu ne da kowa zai iya fahimtar cewa Turkiyya na neman karin tallafi don kula da 'yan gudun hijirar

Sharhi: Bernd Riegert


Ga Tarayyar turai dai tarurrukan ministocin harkokin waje, da ma kafa rundunar dayke shawagi kan teku don hana 'yan gudun hijira shigowa Turai, duk wani munafinci ne. Tun shekaru hudu shugabannin EU sun kwana da tabbacin cewa, yarjejeniya da ke aiki tsakaninsu da Turkiyya dole a nemo mafita.


 EU ta tsara rarraba 'yan gudun hijiran Siriya da Afghanistan da Iran da na sauran kasashen Afirka. To amma akasarin kasashe mambobin EU na kin karban kasonsu na 'yan gudun hijira, misali Poland da Hungari da Ostiriya da Italiya.

A kasashen EU da yawa, an yi ta samun masu tsattsauran ra'ayi da ke kyamar baki, wandanda ke sukar yadda ake barin 'yan gudun hijira a kasashensu. 
 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani