1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Ukraine na ɗaukar sabon salo

March 12, 2014

Shugabanin Turai na cigaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da dambarwar siyasar dake gudana tsakanin Rasha da Ukraine inda suke barazanar ɗaukar matakai masu tsauri

Ukraine pro-ukrainische Demonstration in Simferopol 9.3.2014
Hoto: Reuters

Jamiyyar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta fara samun goyon bayan al'ummar ƙasar sakamakon irin rawar da take takawa wajen sulhunta tsakanin Rasha da Ukraine ta hanyar diplomasiyya. To sai dai ƙasashen yankin Baltic na fargabar cewa yunƙurin ba zai yi tasiri ba domin Rasha tamkar ƙadangaren bakin tulu ne ga Jamus saboda dogaron da take yi da ita dan samun iskar gas.

Tun a jiya talata gwamnatin Ukraine ta yi kira ga ƙasashen yamma da su taimaka mata wajen dakatar da mahukuntan Mosko daga mayar da yankin Kirimiya wani ɓangare na ta sai da mashigin tekun Bahr Aswad na nan maƙare da dakarun Rasha abin da ke nuna alamun wata ƙila Rasha ta fara jagorantar yankin nan da 'yan kawanaki masu zuwa, tunda ma dakarun Ukraine tamkar fursunoni ne a sansanoninsu dake yankin

To sai dai duk da kyakyawar fatan da Ukraine ta nuna tana da shi a ƙasashen yamman Poland da wasu ƙasashen yankin Baltic na damuwar cewa dogaron da Jamus, wadda ake wa kallon mafi ƙarfin tattalin arziƙi a Turai ke yi kan Rasha domin samun makamashi zai iya hana ta ɗaukar irin matakan da suka dace kan Rasha.

Ganawar Merkel da Tusk na EstoniyaHoto: Janek SkarzynskiI/AFP/Getty Images

Merkel na ziyara a ƙasar Poland

A wannan larabar ce Merkel za ta isa Warsaw babban birnin ƙasar Poland, kuma tun ranar litini firaministan ƙasar Donald Tusk ya ce ba zai ɓata lokaci wajen faɗa mata barazanar da wannan lamari ke da shi ga siyasarsu ba domin ba Jamus kaɗe take samun iskar gas ɗin daga Rasha ba

Ko a makon da ya gabata, sai da shugabar ƙasar Lithuania Dalia GRY-Baus-Kaite ta yi Allah wadai da abin da ta kira cin zarafi a bayyane daga ɓangaren mahukuntan na Mosko inda ta ce yi gargaɗin cewa zai yi tasiri sosai a yankin domin a cewarta lamari ne da ya shafi sake shata iyakoki inda take la'akari da yunƙurin Rasha na laƙume har da mashigin Kirimiya

Viktor Yanukovich ya ce yana nan kan matsayinsa

Duk wannan dambarwar da ake ciki hamɓararren shugaban ƙasa Viktor Yanukovich bai sauya tunaninsa ba domin ya bayyana cewa zai koma Ukraine kuma ma ya kwatanta tsige shin da aka yi a matsayin ta'addanci

Hoto: Reuters

Ina so in tunatar muku da cewa muƙami na bai tsaya a halataccen shugaban ƙasa kaɗai ba, ni ne babban kwamandan rundunar sojin ƙasa, kuma ban dakatar da iko na kafin cikan wa'adi ba, ina nan da rai, hanyar da aka bi wajen tsige ni, ya saɓawa tanadin kundin tsarin mulkin Ukraine.

A yayin da lamura ke cigaba da ta'azara, ƙasashen Jamus da Faransa sun ce ba za a daɗe ba zasu ƙaƙabawa Rasha takunkumi, ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius ya ce suna shirin ɗaukar matakan da suka haɗa da ɗora hannu kan kadarorin 'yan Rasha da Ukraine, da haramcin tafiya, waɗanda ma mai yiwuwa su fara aiki a cikin wannan makon.

Manazarta ba su goyi bayan ɓallewar Kirimiya ba

Manazarta dai na ganin cewa rashin ɗaukar matakai masu tsauri kan Rasha zai kasance babban haɗari, domin wajibi ne a kwantata mata cewa mamaye yankin wata ƙasa dake zama mamba a Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma, da Hukumar haɗin kan Turai ta fanin tattalin arziƙi da tsaro wato OSCE, da ma majilasar zartarwar Turai ba abu ne da za a lamunta ba.

A wani yunƙuri na kwantar da hankulan ƙasashen yankin Baltic, a wata ziyara da ya kai ƙasar Estoniya, ministan harkoki wajen Jamus Frank Walther Stenmeier ya ce ƙungiyar EU da ta ƙawancen tsaron NATO za su ba su kariya ta ɗaukar matakan da suka dace

Jirgin ruwan yaƙin Amirka a atisayensu da Bulgariya da RomaniyaHoto: Reuters

Ranar litini idan Allah ya kai mu, ke nan idan har aka wuce ƙarshen mako, kuma Rasha bata sauya matsayinta ba, zamu tattauna matakin da zamu ɗauka a majalisar zartarwar Turai, ko ɗaya bamu su a kai ga yin sa'in sa, amma yadda Rasha ke yi ne ya sa dole mu zauna da shiri abun da ya zama wajibi in ce a halin da ake ciki yana da mahimmancin gaske.

A yanzu haka dai firaministan Ukraine Arseniy Yatsenyuk na hanyar ganawa da shugaba Barack Obama na Amirka domin samun tallafi da goyon baya a rikicin dake tsakanin Gabas da Yamma, wanda ke zaman mafi muni tun bayan yaƙin cacar baki.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Muhammad Nasiru Awal