1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin ya ɓarke bayan dakatar da Siriya a ƙungiyar ƙasashen Larabawa

November 13, 2011

Ana ci gaba da ɗauki ba daɗi tsakanin masu goyon bayan gwamnatin Siriya da masu adawa da ita kwana ɗaya bayan da ƙungiyar ƙasashen Larabawa ta dakatar da ita

Shugaba Bashar al-AssadHoto: picture-alliance/dpa

A ƙasar Siriya dakarun tsaro sun kashe mutane biyar a biranen Homs da Hama a ci gaba da ɗaukar matakan murƙushe masu boren nuna adawa da gwamnati. An kuma samu sojoji biyu da wasu yan bindiga suka kashe bayan da suka yi musu kwantar ɓauna a garin Qusayr dake kusa da Homs da kuma wasu daliban fannin injiniya na jami'ar Baath da suka samu raunuka bayan da aka buɗe wuta akan ginin sashinsu. Hakan dai ya faru ne kwana ɗaya bayan da ƙungiyar ƙasashen Larabawa ta dakatar da Siriya domin ladabtar da ita bisa matakai masu tsauri da take ɗauka domin murƙushe zanga-zangar neman sauyi wadda a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya mutane 3,500 suka rasa rayukansu a cikinta.

A matsayin wani mataki na bayyana fushinsu game da goyon bayan da Turkiya ta bayar ga shawarar da ƙungiyar ƙasashen Larabawa ta dakatar da Siriya dubban 'yan zanga zanga masu goyon bayan gwamnati sun kai ma ofishin jakadancin Turkiya harin. ' Yan zanga-zanga dubu biyar ne dai suka auka wa ofishin jakandicin Turkiya suka kuma farfasa tagogin ginin dake birnin Lattakiya suka kuma kona tutar Turkiya.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Usman Shehu Usman