1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ci gaba da rufe shagunan 'yan Najeriya a Ghana

August 17, 2020

Gwamnatin Najeriya na shirin daukar matakin gaggawa bisa matakin rufe shagunan 'yan kasuwar Najeriya a birnin Accra a Ghana.

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo da takwaransa na Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo da takwaransa na Najeriya Muhammadu Buhari

Duk da cewar suna ikirarin imani da hadewa wuri guda da sunan ciniki a nan gaba, rikici na dada nisan cikin takaddamar ciniki a tsakanin Ghana da tarayyar Najeriya da ke zama na kawaye a cikin yankin yammacin Afirka.

Kuma alamun lalacewar lamuran dai sun faro ne tun bayan matakin mahukuntan tarayyar Najeriyar na rufe iyakokinta da makwabta da nufin kare kanta bisa annobar fasakwabri da ma kwarara ta kanana na makamai cikin kasar. Matakin kuma da ya jefa tattali na arzikin mutanen Accran a cikin yanayi maras kyawu.

Bayan kare lalama da farkon fari dai 'yan kasuwar na Ghana sun rika bi suna tilasta 'yan tiredar Najeriyar rufe shago a watan Disamban bara sakamakon wata dokar da ta gindaya sharuddan ciniki a kasar Ghana.

An dai kai har ga rusa wani gini da ke a harabar offishin jakadancin Najeriyar a birnin Accra duk dai a wani abin da ke nuna alamun lalacewar lamura a tsakani na kawayen guda biyu.

Kokarin aiwatar da wannan doka da ta kunshi biyan haraji na Dala Miliyan daya ga duk wani dan kasuwa na tarrayar Najeriyar da ke da burin ciniki a kasar Ghana dai ya kalli kulle shaguna na 'yan tiredar tarrayar Najeriyar a karo na biyu cikin kasa da tsawo na shekara guda.

Ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya ce kasarsa za ta mai da martani don kare martabar 'ya'yanta da ke GhanaHoto: DW/B. Darame

Matakin kuma da daga dukkan alamu ya bata ran mahukunta a Abuja. Ministan harkokin wajen tarrayar Najeriyar Geoffrey Onyeama dai ya ce "kasar tana shirin mai da martanin gaggawa da nufin kare martaba da kimar 'ya'yanta da ke biranen Ghanan kuma ke gudanar da harkoki na kasuwa a halin yanzu."

Duk da cewar dai ministan bai ambaci irin matakin da Abujar ke tunani da ta dauka da nufin warware rikicin ba, a  fadar Hajiya Saratu Aliyu da ke zaman shugaba ta kungiya ta masu kasuwar tarrayar Najeriyar akwai "bukatar takatsantsan da nufin kaucewa baci na ruwa da ke zama na muhimmi ga kasashen guda biyu."

Sai da ta kai ga tsoma baki na shugaban kasar Ghanan kafin iya bude shaguna na masu kasuwar tarrayar Najeriyar a watan na Disamban da ya shude.

'Yan Ghana dai sun ce dokar kasar ta hana baki yin kananan kasuwanci cikin kasarHoto: AP

To sai dai kuma sake barkewar rikicin na nuna irin jan aikin da ke gaban kasashen Afirka da ke ikirarin ciniki na bai daya amma kuma ke kara tsuke damar baki na taka rawa a tattalin arziki na kasashen.

Da ranar wannan Litinin dai aka kaddamar da hedikwatar kasuwar ta bai daya ta kasashen na Afirka a birnin na Accra a wani abin da ke nuna nisa na tunanin 'yan mulki na nahiyar da ke kallon yunkurin damar habbaka ciniki a tsakanin kasashen, duk da karuwar rikicin da ke a tsakanin talakawa.

To sai dai kuma a tunanin Dr Sani Yandaki da ke zaman masani a cikin harkokin ciniki a nahiyar, har yanzu da "sauran tafiya a tsakanin kasashen da iya kaiwa ga kwantar da hankalin al'umma a kokari na hadewar a cikin sunan ciniki."

Daga ranar daya ga watan Janairu na shekarar badi ne dai aka tsara kaddamar da kasuwar ta bai daya da ke da burin habbaka cinikin da kila sauya makomar al'umma a nahiyar ta Afirka.