Rikicin 'yan Sanda da Lauyoyi a Pakistan
November 5, 2007`Yan sanda a ƙasar Pakistan sun yi amfani da borkonon tsohuwa da kulake wajen tarwatsa gungun lauyoyi masu zanga-zanga a birane aƙalla uku su na masu adawa da dokar ta ɓaci da shugaba Parvez Musharraf ya ayyana a ƙasar.Lauyoyi da dama an bada rahoton sun samu raunuka a karawar da su ka yi da `yan sanda a biranen Lahore da Karachi da Rawalpindi.Yawancinsu kuma an tsare su. Ƙungiyoyin Lauyoyi da na kare hakkin bil adama ne su ka kira wannan zanga-zanga domin nuna ƙin amincewarsu da dokar ta ɓaci da shugaban ƙasar ya kafa a ranar Asabar.Daruruwan `yan adawar gwamnati kuma an tsare su,inda kuma mataimakin firaminista Shaukat Aziz ya ce mai yiwuwa ne a dakatar da zaben `yan majalisa da a ka shirya gudanarwa a watan Janairu.Ƙasashen Amurka da Burtaniya a halin yanzu sun yi kira da komawa dokokin tsarin mulki tare kuma da gudanar da zaɓe a watan Janairu kamar yadda aka tsara.A halin da ake ciki kuma gwamnati ta ƙaryata raɗe-raɗin da ke yaɗuwa cikin ƙasar cewa mataimakin babban hafsan sojojin ƙasar ya yi wa Musharraf ɗaurin talala.