1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin yankin Gabas ta Tsakiya

January 16, 2011

Isra'ila na neman izinin tada gine-gine a ɗaya daga cikin matsugunen ta da ke gabashin birnin Qudus

Tattaunawar sulhu tsakanin Palasɗinu da Isra'ilaHoto: picture-alliance/dpa

Wani gidan radion sojoji a Israila ya rawaito cewa Israela na sa ran samun izinin gina gidaje aƙalla 1400 a gabashin birnin Qudus, a wani matsuguni mai suna Gilo wanda ke kusa da Bethlehem. Ana sa ran cewa hukumar da ke kula da tsare-tsaren gine-ginen zata yanke shawarar yin hakan a ranar 24 ga wannan watan.

Wata sanarwa da hukumomi a birnin Qudus suka fitar, ta bayyana cewa bisa tanadin doka, wajibi ne su tattauna a kan tayin ginin saboda 'yan kasuwa masu zaman kansu ne suka miƙa tayin.

Babban kotun duniya dai ta ce Israela ta giggina matsgunen na ta ne bada izini ba.

Palasɗinu na san gabashin Qudus wanda Isra'ila ta anshe tare da yankin gaɓar tekun Jirdan domin su zamar da ita babbar birnin yankin. A ɗaya ɓangaren kuma Isra'ila ta ɗauki Qudus a matsayin babbar birnin ta, lamarin da al'ummomin ƙasa da ƙasa basu amince da shi ba.

Kawo yanzu an ka- sa cin nasara wajen cigaba da Tattaunawar sulhu tsakanin Israela da Palasɗinu dangane da gine-ginen da Israela ke yi a yankin gaɓar tekun Jordan da ke gabashin birnin Qudus.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Ahmed Tijjani Lawal