Rikicin yankin gabas ta tsakiya
December 14, 2010Shugaban yankin Falastinu Mahmud Abbas ya gana da manzon Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya George Mitchell a birnin Ramallah, inda ya buƙaci sanin ko Amurka ta amince da ƙaidojinta kafin ta shiga shirin samar da wata yarjejeniya.
Duk da cewa Isra'ila ta yi maraba da shawarar gudanar da tattaunawar da ba ta gaba da gaba ba, Falasɗinu bata amince ko za ta shiga tattaunawar ba, inda ta haƙiƙance cewar ba za ta shiga wata yarjejeniya ba sai sanda Isra'ila ta daina gine-gine a gaɓar tekun Jordan.
Bayan tattaunawar ta Ramallah, jami'an Falasɗinu sun ce Mitchell ya bayar da shawarwarin yadda za'a cigaba da gudanar da tattaunawar samar da zaman lafiya a yankin, amma bai fito fili ya yi bayani dalla dalla ba, saboda haka za su jira a kammala taron ministocin harkokin wajen ƙasashen Larbawa, wanda za'a gudanar a gobe Laraba a birnin Alkahira.
Tun a jiya ne dai, Mitchell ya gana da frime Ministan Isra'ila, inda ya nuna gamsuwar sa da shawarar Amurka na mayar da hankali a kan mahimman abubuwan da suka haɗa da shata iyakokin ƙasashen biyu, da makomar birnin Qudus a maimakon mai da hankali a kan gine-ginen na Isra'ila.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar