1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin zaɓe a Zimbabwe

Usman ShehuAugust 1, 2013

Ƙasar na daf da faɗawa cikin wani sabon rikici na siyasa bayan sanarwar da jam'iyyar ZANU PF ta bayar cewar ta samu nasara kafin ma hukumar zaɓen ta bayyana sakamakon.

Zimbabwe's President Robert Mugabe addresses a media conference at State house in Harare, on the eve of the country's general elections, July 30, 2013. Heavily armed riot police deployed in potential election flashpoints in Zimbabwe on Tuesday on the eve of a poll showdown between Mugabe and Prime Minister Morgan Tsvangirai that remains too close to call. REUTERS/Philimon Bulawayo (ZIMBABWE - Tags: POLITICS ELECTIONS)
Hoto: Reuters

Shugabar hukumar zaɓen Rita Makarau ta ce suna ci gaba da tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasar zagaye na farko wanda za su bayyana a nan gaba kaɗan. Wanda kuma idan har ba wanda ya samu kishi 50 cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa tsakanin 'yan takarar biyu wanda ake jin ke kan gaba wato Robert Mugabe da kuma Morgan Tsvgirai, to kam sai an kai ga shirya zagaye na biyu a ranar 11 ga watan Satumba da ke tafe.

Ana cikin haka ne kwatsam wani ƙusa a jami'iyyar ta ZANU-PF ya sanar da cewar sun samu nasara kuma sun doke  jam'iyyar MDC, abin da Tsvangirai ya ce ba gaskiya ba ne a cikin wani taron manema labarai da ya yi.

Ya ce : '' Wannan shi ne ra'ayin mu wannan zaɓe ba shi da tushe, da shi da banza duk ɗaya  saboda ba abin da jama'a suka zaɓa ba ne, kuma ya saɓama ƙaidoji SADC da AU.''

An baza 'yan sanda a kusa da jam'iyyar MDC

Yanzu haka dai an baza ɗarurruwan 'yan sanda a kusa da cibiyar jam'iyyar fira ministan wanda tun da farko kafin zaɓen ya yi ƙorafin cewar a kwai alamun yin maguɗi da aka shirya. Rugare Gumbo shi ne kakakin jam'iyyar ta ZaNU PF ya kuma yi watsi da zargin.

Morgan TsvangiraiHoto: Reuters

Ya ce : '' Ta ƙaƙa za mu yi maguɗi wani salo ne na rage martabar zaɓen, daman Amirka da Ingila suna son haka, ya ce wannan wani abu ne da ke da kamar haɗin baki.''

An samu kura-kurai a zaɓen kamar yadda wasu cibiyoyi suka gano.

Tun da fari dai kusan dukkanin wakilai na ƙungiyar Tarrayar Afirka sun yi imanin cewar zaɓen ya gudana cikin haske da addalci kafin ƙungiyar SADC ta bayyana sakamakonta na saka ido a gobe Jumma'a. To amma wata jami'ar wata ƙungiyar kare hakin bil adama ta Zimbabwe Irene Petras ta ce akwai kura-kurai.

Masu kaɗa ƙuri'aHoto: Alexander Joe/AFP/Getty Images

Ta ce  :'' Abin da za mu iya cewa shi ne a kwai matsaloli da dama abubuwan ba su gudana ba kamar yadda ake so ba, mutane da dama ba su kaɗa ƙuria' ba a zaɓen amma yanzu za mu jira mu ga sakamakon da hukumar zaben za ta bayyana a lokacin za mu iya bayyana r'ayin mu.''

A zaɓen shekara ta 2008 ma sai da ƙungiyar SDAC ta shiga tsakani domin kiyaye ƙasar ga afkawa cikin yaƙin basasa bayan da jam'iyyar ZANU PF ta samu nasara. Robert Mugabe dai na a kan karagar mulkin tun a shekarun 1980 kafin ya raba mulki da fira ministan a shekarun 2009 wato Morgan Tsvangirai a kan matsin lamba na ƙasashen duniya.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita        : Mohammad Nasiru Awal