1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Zaɓen Liberia ya salwantar da rayuka uku

November 7, 2011

'yan sandan Liberia sun yi amfani da ƙarfi wajen tarwatsa gangamin nuna goyon baya ga Tubman da zai ƙaurace ma zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasa. Mutane uku zuwa hudu ne suka mutu a rikicin da ya gudana a Monrovia.

Magoya bayan Sirleaf sun yi alƙawarin fitowa don kaɗa ƙuri'a.Hoto: DW

Aƙalla mutune uku zuwa huɗu sun rasa rayukansu a Monrovia babban birnin Liberia lokacin da 'yan sanda suka yi amfani da ƙarfi wajen tarwatsa gangamin nuna goyon baya ga ɗan takaran da ya ƙaurace ma zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasa da zai gudana ranar talata idan Allah ya kaimu. 'yan sanda sun yi amfani da kulake da kuma borkono mai sa hawaye a cibiyar jam'iyar adawa ta CDC inda ɗaruruwan magoya bayan Winston Tubman suka yi taru domin yin Allah wadai da abin da suka danganta da maguɗin zaɓe.

Shi dai Winston Tubman na jam'iyar CDC da ya kamata ya kamata ya ƙalubalanci shugaba mai barin gado, ya zargi Ellen Johnson Sirleaf da tafka murɗiya a zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana ranar 11 ga watan oktoba. Ana sa ran Ellen Johson Sirleaf da ta zo na ɗaya a zagayen farko za ta haye ba tare da wata matsala ba. sai dai kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa na nuna fargaba game da yiwuwar ɓarkewar tashin hankali a Liberiar da ta taɓa ɗanɗana raɗaɗin yaƙin basasa na shekaru huɗu wanda ya salwantar da rayuka dubu 250.

Dakarun Majalisar Ɗinkin Duniya sun shiga tsakanin ɓangarorin biyu domin gujewa duk wata tashin tashina a daidai lokacin da ake shirin kaɗa ƙuri'a.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu