1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Ko an kafa EFCC a kan doka?

Uwais Abubakar Idris L
October 17, 2024

Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Najeriya Zagon Kasa (EFCC), na fuskantar tuhuma kan halaccinta a matsayin hukuma.

Najeriya | EFCC | Tattalin Arziki
Rikici kan halaccin hukumar EFCC ta Najeriya, na kara kamariHoto: Ubale Musa/DW

Bayan kwashe shekaru 21 da kafuwar Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Najeriya Zagon Kasa (EFCC) ne, wannan sabuwar takaddama ta kuno kai game da halaccinta. Masu korafi na bukatar a fayyace dokokin da suka kafa ta, domin akwai masu ganin cewa ba a bi dokokin tsarin mulkin kasar wajen kafa hukumar ba. Kama daga kotun kolin Najeriyar, inda manyan alkalai ke bibiyar karar da wasu gwamnoni 15 suka kai a kokarinsu na yanke hukunci a ranar 22 ga wannan watan, shi ma tsohon shugaban kungiyar Lauyoyi ta Najeriya Olisa Gbakoba ya aike da koke ga majalisun dokokin kasar, inda ya ce an saba doka wajen kafa hukumar.

Ba wannan ne karon farko da ake samun cece-kuce kan hukumar ta EFCC ta Najeriya baHoto: DW/ A. Baba Aminu

Duk da dimbin kararraki na tuhumar wadanda ake zargi da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin Najeriyar zagon kasa, tare da samun nasarar kwato makudan kudi da aka diba ta haramtaciyyar hanya, hukumar ta EFCC ta yi kaurin suna wajen binciken wadanda gwamnatin da ke mulki ke fushi da su. Wannan ya sanya ana yi mata kallon karen farautar gwamnati, inda tuni kungiyoyin farar hula suka shiga lamarin. Barrsiter Mainasara Umar Kogo Faskari ya bayyana bukatar wankan tsarki ga hukumar ta EFCC, ta hanyar fara hukunci daga gida. Hukuncin da kotun kolin Najeriya za ta yanke a kan makomar hukumar ta EFCC a ranar 22 ga watan nan, zai share fage wajen fahimtar matakin da majalisar dokokin za ta dauka a kan batun domin gane ko gwamnononin da suka kai kara sun yi ne don kaucewa bincike.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani