1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikita-rikitar siyasa a Nijar

Gazali Abdu TasawaDecember 8, 2014

A Jamhuriyar Nijar babban taron kasa karo na biyu na jam'iyyar Lumana Afrika, ya kara zabar Malam Hama Amadou a matsayin sabon shugaban jam'iyyar na kasa baki daya.

Hoto: DW/S. Boukari

Babban taron jam'iyyar wanda ya samu halartar dubban 'ya'yanta na ciki da wajen kasar dama shugabannin jam'iyyun adawa, ya zo ne a daidai lokacin da shugaban jam'iyyar ke zaman gudun hijira. An dai yi ta rera wakoki masu dauke da habaici a yayin taron na Lumana Afirka da ya yi bitar rayuwar jam'iyyar.

Amfani da kafafen sadarwa na zamani

Malam Hama Amadou wanda a yanzu haka ya ke gudun hijira dai ya gabatar da jawabi ga dubban 'ya'yan jam'iyyar da suka halarci taron ta hanyar amfani da kafar sadarwa ta Internet, inda ya yi amfani da majigin da ake wa lakabi da "Video Conference". Taron jam'iyyar ta Lumana Afirka dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da aka fara samun wata sabuwar baraka a cikin jam'iyyar reshen birnin Yamai da ke zaman babbar cibiyarta bisa abin da ake dangantawa da rikicin shugabanci.

Masu kada kuri'a a NijarHoto: AP
Zaman majalisar dokoki a NijarHoto: DW/M. Kanta

Ya da kwallon mangwaro

An dai kammala wannan babban taro na Lumana Afirka, ba tare da 'ya'yanta da uwar jamiyyar tasu ta kora sun halarta ba, inda tuni wasu daga cikinsu irinsu Malam Sala Habi su ka ce sun yada kwallon mangwaro domin su huta da kuda, ta hanyar kafa tasu sabuwar jamiyya. Abun jira a gani dai shine yadda shugaban jamiyyar Malam Hama Amadu da ke gudun hijira zai gudanar da takararsa a zabuka masu zuwa.