1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rincabewar rikicin Siriya

July 31, 2012

'Yan tawayen Siriya sun kai samamen daya janyo mutuwar 'yan sanda 40 a birnin Aleppo.

epa03318505 Syrian rebels patrol near Aleppo, Syria, 26 July 2012. According to media reports, Syrian rebels and government forces on 26 July 2012 fought fierce battles for control of Syria's two largest cities of Damascus and Aleppo, opposition activists said. EPA/SINAN GUL/ANADOLU AGENCY TURKEY OUT HANDOUT EDITORIAL USE ONLY/NO SALES/NO ARCHIVES +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

A yayin da fada mai tsanani ya shjiga yini na hudu a birnin Aleppo dake zama cibiyar kasuwancin kasar Siriya, kungiyar dake fafutukar kare hakkin jama'a a kasar, ta sanar da cewar a wannan Talatar ce 'yan tawaye suka kaddamar da hare hare akan wasu caji-ofis biyu, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar kimanin jami'an 'yan Sanda 40. A cewar Rami Abder Rahman, darektan kungiyar kare hakkin bil'Adamar wadda tushen ta ke kasar Birtaniya, daga cikin mamatan, harda shugaban 'yan Sanda na unguwar Salhin dake kudancin birnin na Aleppo, yayin da kuma 'yan tawayen suka lalata wasu motoci ukku.

Kungiyar kare hakkin bil'adamar ta kuma ce akwai wani fadan daya barke a birnin Zarhraa dake yankin arewacin kasar, inda 'yan tawayen suka kaddamar da hari akan ofishin hukumar leken asirin kasar ta Siriya - reshen yankin.

A halin da ake ciki kuma sabon mai shiga tsakani na Majalisar Dinkin Duniya a rikicin na Siriya ya ce ko da shike akwai kudirin da dukkan sassan dake cikin rikicin na Siriya suka nuna amma sai ya gani a kasa tukuna:

Ya ce "Ba kowanne daga cikin bangarorin biyu daya ce a'a ga batun tsagaita bude wuta da kuma kulla yarjejeniya, amma idan har ba'a kammala hakan ba, kuma al'umma ta ga ci gaba mai ma'ana a kasa, to, kuwa zai ci gaba da kasancewa fata ne, domin kuwa na yi imani da ganin sakamako - a aikace."

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu