1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za mu daukaka kara kan batun Ruwanda

Lateefa Mustapha Ja'afar
June 29, 2023

Firaministan Ingila Rishi Sunak ya bayyana cewa gwamnati za ta daukaka kara zuwa kotun koli, dangane da batun masu neman mafaka a Birtaniya da ake kokarin mayar da su Ruwanda tare da ayyana Kigalin da tudun mun tsira.

Birtaniya | Masu Neman Mafaka | Ruwanda
Kungiyoyi kare hakkin dan Adam, na adawa da kai masu neman mafakar RuwandaHoto: Niklas Hallen/AFP/Getty Images

Bayanin na Firaministan Rishi Sunak na zuwa ne bayan da wata kotun daukaka kara ta yanke hukuncin haramta mayar da masu neman mafakar zuwa Ruwanda, bayan da alkalai uku suka bayyana cewa har sai an yi gyara a dokokin neman mafaka na Kigalin kafin ta iya zama tunudn mun tsiran. Wannan dai na nuni da cewa, sun aminta da kokken masu neman mafakar da kuma kungiyoyin da ke ba su kariya da suka gurfanar da gwamnatin Birtaniyan a gaban kuliya.