1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rishi Sunak ya zama sabon firaministan Birtaniya

Mouhamadou Awal Balarabe
October 25, 2022

Sarkin Ingila Charles III ya bai wa Rishi Sunak damar kafa gwamnati a hukumance, lamarin da ya ba shi damar zama firaministan Birtaniya na uku a cikin watanni biyu, a kasar da ke fama da mawuyacin hali na tattalin arziki

König Charles III  Rishi Sunak
Hoto: Aaron Chown/AP/picture alliance

Shi dai Rishi Sunak da ke zama tsohon ma'aikacin banki kuma tsohon ministan kudi, ya zama firaministan Birtaniyya na farko dan asalin Indiya mai bin addinin Hindu. kuma na farko da ya fito daga tsohuwar kasa da Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka. Jagoran mai shekaru 42 da haihuwa, ya kasance shugaban gwamnati mafi karancin shekaru a tarihin kasar Birtaniya.

Amma Rishi Sunak ya yi watsi da zaben gaba da wa'adi ko zaben wuri, wanda jam'iyyar Labour ta nemi a gudanar. Ya hau kan kujerar tafiyar da gwamnatin Birtaniya ne, a wani yanayi na tabarbarewar zamantakewa da aka jima ba a ga irinsa ba a kasar. Sunak ya zama firaministan Birtaniya na biyar cikin shekaru shida, wato lokacin da kasar ta zabi a zaben raba gari da Kungiyar Tarayyar Turai, kuma na uku cikin watanni biyu.