Sabuwar rigima ta barke a siyasar Jihar Rivers
October 26, 2026
Bayanai sun ce an samu rashin jituwar ce a taron sulhu, bayan wani rikici da ya shafi ɗan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar APC, Kingsley Chinda da kuma Gwamnan, inda magoya bayan Fubara ke duba yiwuwar ficewa daga ƙungiyar kawance ta "Rainbow Coalition" zuwa jam'iyyar African Democratic Congress, ADC.
Wannan sabuwar takaddamar na gwada ƙarfin fahimtar juna tsakanin Wike da Fubara, waɗanda rikicinsu na siyasa ya yi tasiri sosai kan siyasar jihar Rivers tun shekarar 2023.
Duk da cewa tarukan sulhun da aka yi ta gudanarwa a baya sun haifar da fatan samun matsaya guda, sai dai abubuwan da ke faruwa yanzu na nuna har yanzu akwai sabani kan iko da wakilci da kuma makomar ƙungiyar kawancen da Nyesom Wikeya kafa kuma ya ke jagoranta.
A taron bangarorin biyu a ranar lahadi, Wike da kansa ya gwaba wa wasu kusoshi magoya bayan Fubara magana, sannan dan takarar gwamna na yanzu, da Wike din ya kafa, wato Kingsley Chinda ya ce kada a sake kiran Sim Fubara jagoran siyasar jihar Rivers, lamarin kuma da bai yiwa magoya bayan Fubara din dadi ba, dama har yanzu suna kokarin tantance makomar su ta siyasa a sabon tsarin hadaka na "Rainbow Coalition".
Sakamakon wannan yanayi, yanzu tambayar ita ce ko magoya bayan gwamna Fubara da kuma ƙaƙƙarfan tsarin siyasar Wike za su kai ga iya yin aiki tare a ƙarƙashin ƙawancen siyasa guda, ba tare da kowanne ɓangare ya ji an tauye masa hakkinsa na siyasa ba.
Nyesom Wike dai na da kyakkyawar alaƙa da 'yan majalisar dokokin jahar, da shugabannin ƙananan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki a siyasar jihar ta Rivers. Inda Shi kuma gwamna Fubara ke da nasa magoya bayan, waɗanda muradunsu ba lallai ne su yi daidai da na tsohon gwamnan ba. Fitowar Kingsley Chinda a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar APC a zaɓen 2027, ta ƙara wani sabon salo ga wannan siyasa, musamman a yayin da masu ruwa da tsaki ke ƙoƙarin tabbatar da matsayinsu a cikin ƙungiyar ta Rainbow.
Yanzu dai babban batun shine cewa wasu magoya bayan Fubara na tunanin komawa wata jamiyyar ta daban wato ADC, wadda hakan ke dada fito da rashin gamsuwar su karara da tsarin siyasar da ake bi ta rainbow coalition.
Ga Wike dai, babban ƙalubalen shi ne yadda zai tabbatar da haɗin kan ƙungiyoyin da ke goyon bayan Rainbow Coalition.
Ga Fubara kuwa, abin dubawa shi ne ko magoya bayansa za su ci gaba da amincewa da tsarin siyasar da faruwa a ƙarƙashin sulhun.
Taron sirri da aka nuna za a gudanarwa tsakanin bangaren Wike da na Fubara a nan gaba an nunar zai iya ba wa ɓangarorin biyu damar tattauna matsalolinsu da ta hada da fayyace yadda kowane bangare zai taka rawar siyasa.
Yayin da zaɓen 2027 ke ƙaratowa, Rainbow Coalition na cikin ƙawancen siyasa da ke da alaƙa da ƙoƙarin sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu da kuma fafatawar neman tasiri a yankin Neja Delta.
A halin yanzu, makomar Rainbow Coalition ta Nyesom Wike, ta zama abin da ake bibiya sosai a siyasar jihar Rivers.