Roberts Gates ya ce dabarun yaƙin Amurka a Kandahar na tasiri
September 3, 2010Talla
Sakataren tsaron Amurka Robert Gates ya bayyana cewar ya ga alamun da ke tabbatar da cewar dabarun Amurka a Afganistna yana yin tasiri a lardin Kandahar mai fama da rigingimu.
Gates ya yi wannan furucin ne bayan rangadin sansanoni da ganawa da Dakarun Amurka a birnin na Kandahar da ke zama maɓuyan 'yan Taliban, kuma inda suke cigaba da yaƙar sojojin haɗakar.
Sakataren tsaron Amurkan ya kasa ɓoyewa 'yan jarida farin cikinsa a dangane da abun da ya kira Nasarar da dakarun Amurkan da na ƙungiyar tsaro ta NATO ke samu akan mayaƙan Taliban a fafatawar da ke gudana tsakanin ɓangarorin biyu a Kandahar.
Mawallafiyya: Zainab Mohammad Abubakar
Edita: Abdullahi Tanko Bala