Burkina: Shugaba Kaboré ya karbi wani wa'adin mulki
December 28, 2020Talla
Roch Marc Christian Kaboré mai shekaru 63 a duniya a cikin jawabinsa a gaban jama'a ciki har da takwarorinsa na wasu kasashen Afirka, yayi alwashin aiki tukuru domin ganin ya hada kan 'yan kasar a cikin sabon wa'adin mulkin da aka rantsar da shi na shekaru biyar.
Shugaban ya ce bayyana anniyarsa ta kafa wani sabon kwamitin tuntubar juna daga farkon wa'adinsa na biyu, a wani mataki na kawo karshen zubar da jini, da hasarar dukiyar kasa da kuma rudanin siyasar da shugaban yace tun bayan samun 'yancin kasar zauke yanzu ta ke hadasa illa tsakanin 'yan kasar.