1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaMasar

Hare-haren rokoki a iyakar Masar da Isra'ila

October 27, 2023

Akalla mutane shida sun samu raunika a wani gari da ake kira Taba da ke iyakar Masar da Isra'ila bayan fadowar wasu makaman roka.

Vorschaubild Explainer | Arab Neighbors
Hoto: DW

Wasu majiyoyi da ke yankin sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewar makaman rokan sun fado ne a wani asibitin garin dake gabar Tekun Bahar Maliya wanda ke raba iyakokin Masar da Isra'ila daga Arewa maso gabashin birnin Sinai.

Karin bayani: Isra'ila ta jikkata sojan Masar a iyakar Gaza

Masar dai da ke a sahun farko na shiga tsakani a rikiciki tsakanin kungiyar Hamas da Isra'ila kuma ke zama kofa ta shigar da kayan agaji i zuwa zirin Gaza ta tsinci kanta cikin tsaka mai wuya tun a ranar bakoye ga wannan wata na Oktoba a daidai lokacin barkewar sabon tashin hankalin.

Karin bayani: Masar ta shirya taron zaman lafiya kan rikicin Gaza

A baya dai shugaban kasar Abdel Fattah al-Sissi ya bukaci dakarun kasar dake Suez da su kasance cikin shirin ko ta kwana tare kuma da kiran bangororin da ke rikici da su rinka sara suna duba bakin gatari.