Romano Prodi ya ƙetara rijiya da baya
March 1, 2007Talla
Shugaban gwamnatin Italia Romano Prodi, ya ƙetara rijiya da baya,a sakamkon ƙuri´ar da yan majalisar wakilai su ka kaɗa jiya, wadda kuma ta bashi damar ci gaba da jagorantar gwamnati, bayan murabus ɗin da yayi a makon da ya gabata.
Sakamakon ƙuri´un ya nunar da cewa yan majalisa 167 su ka amince, a yayin da 157 su ka hau kujera naƙi.
Gobe idan Allah ya kai mu, ita ma majalisar dattawa, za ta kaɗa ƙuri´a, to saidai a nan, Prodi ba shi da faɗuwar gaba ta la´akari da babban rinjayen rukunin jam´iyu, masu bashi goyan baya.
A jawabin da ya yi wa ga yan jarida, jim kaɗan bayan bayyana sakamakon , Romano Prodi, ya alkawarta duƙƙufa kan aiki, tare da haɗin kan al´umomin ƙasar Italia, da a halin yanzu siyasa ta rarraba.