Iran: Zargin kashe masu zanga-zanga
November 20, 2019Talla
Kafar yada labaran gwamnatin Iran din ce ta yada jawabin da shugaban kasar ya yi, a daidai lokacin da dubban mutane suka fantsama kan tituna domin yin zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati dangane da matakan da ta dauka na kara farashin man fetur.
Wannan lamari dai na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyoyin kare hakkin dan Adam irinsu Amnesty International ke cewa sama da mutane 100 suka halaka a yankuna daban-daban na kasar, a kokarin murkushe masu zanga-zangar.