Rowhani ya lashe zaɓen shugabancin Iran
June 15, 2013Ɗan takaran zaɓen shugaban ƙasa a Iran Hassan Rowhani mai matsakaicin ra'ayin riƙau ya lashe zaɓen da a ka gudanar a ranar juma'a. Ministan kula da harkokin cikin gidan ƙasar ne ya bada wannan sanarwa, wacce ta kawo ƙarshen mulkin masu ra'ayin riƙau na tsawon shekaru takwas. Kamfanin dillancin labarun AFP na Faransa ya rawaito cewa dubban magoya bayan shugaban mai jiran gado sun yi maci zuwa dandalin Vali-Asr suna ɗauke da hotunan Rowhani suna kuma raira baitocin da ke karrama shi.
Fiye da kashi 70 na mutane milliyan 50 da suka cancanci kaɗa ƙuri'a suka yi zaɓe, haka nan kuma sakamokon zaɓen ya bayyana Mohammed Baqer Qalibaf magajin garin Tehran a matsayin wanda ya zo na biyu a yayin da Saeed Jalili, babban wakilin da ke shiga tsakanin tattaunawar makamashin nukiliyar ƙasar ya zo na uku da kusan kashi 11 cikin ɗari na yawan ƙuri'un da aka kaɗa. Tuni dai wasu daga cikin 'yan takaran suka nuna amincewarsu da wannan sakamako suka kuma amince sun sha kaye.
Ɗaya daga cikin manyan 'yan adawan ƙasar da ke gudun hijira Ardeshir Amir Aarjomand ya yi maraba da wannan nasara na Rowhani. Sai dai ya yi gargaɗin cewa ko da shi ke mafi yawan magoya bayansa ma su neman sauyi ne, ya na da kyakyawar dangantakar addini da sansanin Qom, wanda a ka bayyana shi a matsanin sansani mafi ƙarfi na addini a ƙasar .
Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe