1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

RSF ta halaka fararen hula da dama a Sudan

September 10, 2024

Dakarun rundunar kar-ta-kwana ta RSF a Sudan sun kaddamar da mummunar farmaki a wata kasuwa da ke birnin Sennar a kudu maso gabashin kasar, inda shaidun gani da ido ke cewa harin ya halaka kimanin mutane 30.

Wata kasuwa da dakarun RSF suka kona a 2023 a El Fasher na yankin Dafur a Sudan
Wata kasuwa da dakarun RSF suka kona a 2023 a El Fasher na yankin Dafur a Sudan Hoto: AFP

Sennar ya kasance yanki daya tilo da ke karkashin ikon dakarun gwamnatin Abdel Fattah al-Burhan a kudu maso gabashin Sudan, da suka shafe sama da watanni 16 suna gwabza yaki da mayakan RSF. Wata sanarwa da Kungiyar lauyoyin Sudan ta fitar ta ce harin ya halaka fararen hula 31 yayin da wasu sama da 100 suka jikkata a kasuwar ta Sennar.

Karin bayani: Sudan ta zargi UAE da rura wutar rikicin yakin basasar kasar

Harin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun rahotannin tashin hankali a birnin El-Fasherda ke arewacin lardin Dafur, karkashin ikon Mohamed Hamdan Daglo, shugaban rundunar RSF wanda suka raba-gari da shugaban gwamnatin sojin kasar Janar Abdel Fattah al-Burhan.