RSF ta kwace iko da hedikwatar sojoji ta al-Fashir
October 26, 2025
Mayakan RSF na Sudan sun ce sun kwace ikon hedikwatar sojoji ta kasar da ke birnin al-Fashir. Wani faifan bidiyo da RSF ta wallafa da kamfanin dillancin labaran Reuters ya tabbatar da wurin, ya nuna yadda mayakan ke ta murna.
Karin bayani: RSF ta kai hari da jirgi maras matuki a El-Fashir na Sudan
Kawo yanzu dakarun sojin kasar ba su ce uffan ba a kai ba. Kwace iko da al-Fashir na nuna wata gagarumar nasara ga RSF wanda zai iya kai ga gaggauta raba kasar, ta hanyar ba wa kungiyar ta sa kai damar karfafa iko da babban yankin Darfur. Tun da fari wasu na ganin cewa idan RSF ta kwace iko da birnin, zai iya haifar da rikicin kabilanci kamar yadda aka gani bayan ta kwace iko da sansanin Zamzam da ke kudancin kasar.
A watan da ya gabata ne kuma Majalisar Dinkin Duniya ta zargi RSF da aikata laifukan cin zarafi yayin da suke yi wa birnin na al-Fashir kawanya, inda dakarun Sudan suka zarge su da aikata laifukan yaki.