Ruɗani a kan batun sace mata da yara a Damasak
March 25, 2015Rahotannin da ke nuna cewar an ɗauke mata da yara sama da 500 a Damasak da ke jihar Borno a yankin Arewa maso gabashin Najeriya ya cika kafafen yaɗa labarai na cikin gida da ma manyan kafafen yaɗa labarai na ƙasashen waje.Sai dai bayyanai da ke fitowa daga wannan garin da dakarun Najeriya da ƙawayensu na ƙasashen Nijar da Chadi da Kamaru suka ƙwato a makon da ya gabata na nuna cewar akwai ruɗani dangane da labarin sace waɗannan mata da yara.
Babu tabbas dangane da mokamar zra da matan 500 da aka sace
Bayaynai dai sun nuna kafin dakarun Sojin Najeriya da na ƙawance su karɓo garin mayaƙan ƙungiyar sun kwashe iyalansu da kuma waɗanda suka amince su bi su daga garin zuwa wasu sansannoninsu. Wani babban jami'in karamar hukumar Damasak wanda bai so a bayyana sunan sa ko kuma a naɗi muryarsa ba ya bayyana cewar su kan ba su da wannan labari na sace mutane sama da 500.
Jama'a na yin ɗari-ɗari da batun wanda ke ɗaukar hankali duniya
Na kuma tambayi wani bawan Allah wanda garinsu ke kusa da Damasak ya kuma shaida mani ta wayar tarho cewar sun samu labarin a baya kafin karɓar garin an sace mata da yara amma dai ba su tabbata ba.Tun lokacin da ƙungiyar Jama'atu Ahlul Sunna da aka fi sani da Boko Harm ta karɓe iko da garin Damasak ɗaukacin al'ummar da ke da sauran shan ruwa suka tsere inda aka bar mata da yara da tsofaffi.
A halin da ake ciki dai ƙungiyoyi masu fafutuka da na farar hula na ta ƙara yin matsin lamba ga gwamnatin Najeriya da ta ci gaba da yin bincike domin gano waɗannan yara da mata kusan 500 waɗanda ake kyautata zaton cewar watakila tashin hankalin ya rutsa da su.