SiyasaIsra'ila
Marco Rubeo ya gana da Netanyahu
September 15, 2025
Talla
Firaministan na Isra'ila ya yaba wa Amurka Sannan ya kara da cewar kasarsa ke da alhakin kai harin kan Qatar
"Na sha nanata cewa matakin da Isra'ila ta dauka kan shugabannin 'yan ta'addar Hamas a Qatar, mataki ne mai cin gashin kansa na Isra'ila. Wannan shawara ce da ni da manyan jami'an tsaronmu muka dauka. Mune muka gudanar da shi, kuma mun dauki cikakken alhakinsa, saboda mun yi imanin cewa bai kamata a bai wa 'yan ta'adda mafaka .''
Amurka dai na nuna kin amincewa da aniyar wasu kasahen duniya na kafa kasar Falasdinu. Sakataran harkokin wajen Amurkan Marco Rubio na yin ziyara ne. a Isarailar domin jaddada goyon bayan Amurka a kann wannan batu: