Rudani a jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya
December 5, 2014Kasa da tsawon watanni uku da fiskantar 'yan kasar da nufin gwada sa'a dai, alamun ta yi tsami na kara fitowa fili a cikin jam'iyyar da ta zauna ta kalli shugaban da ke kai yanzu ya dakatar da mutumin da ya gada a gadon mulki, da ma karuwar barazanar karon batta a tsakanin tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo da kuma yaron da ya dora Dr Ebele Jonathan.
Dr Umar Ardo dai na zaman wani dan jam'iyyar da kuma shi ma ya zarce ya zuwa kotun koli domin ja da shugaban kasar, kuma a fadarsa daukacin rigingimun PDP na da ruwa da ma tsaki da son rai ne da rashin sanin mutuncin doka a cikin harkokin tafiyar da jam'iyyar
“Abun da ya ke faruwa cikin jam'iyyar PDP rikici ne na wadanda ke son zuciya da suka mayar da harkar jam'iyya kamar nasu da ma harkar kasa kamar nasu. Hakkin jama'a an jefar da shi a bayan gida shi ne rikicin mu na PDP. Rigirmar kuma duk a kan shugaban kasa ne in har shari'ar da na kai kotu ta yanke hukuncin cewar a kau da shugaba Jonathan a kawo wani dan takara to akwai sauran rina a kaba ke nan. Ina zaton PDP za ta iya cigaba da mulki in ba shugaba Jonathan."
Adawar yanzu babbar barazana ce ga PDP
Rikicin na cikin gida game kuma da nuna alamun karin karfi ta adawar da tuni ta fidda nata gwanayen a cikin halin sanyi a mafi yawan jihohi na kasar dai daga dukkan alamu na kara tada hankalin masu gidan na wadata da ke fatan cin moriyar rigingimun cikin gidan abokai na hammayarta.
Tuni dai bakin alkalami ya kama hanyar bushewa ga jam'iyyar da ta ce ko ruwa ko iska ta hada hanya da Ebele da nufin sake daukarta zuwa hanyar da ke cike da kayoyin siyasa a kasar.
To sai dai kuma a fadar Barrister Abdullahi Jalo da ke zaman mataimakin kakakin jam'iyyar na kasa wai fa har yanzu PDP na da sauran karfi kuma na shirin buge yan yara duk da yawan jinin da ke neman rinjayarta kasa
“Ka ga maganar shugaban kasa da Obasanjo, shi kansa shugaban kasar ne ya ce a bar shi ya maida martani da kansa, maganar Bamanga da Mu'azu kuwa magana ce ta kotu, kuma ni ba zan sa baki kan harkar kotu ba. Amma dai ka sani PDP na nan na gudanar da al'amuranta ba kuma ta wargaje ba”
Abun jira a gani dai na zaman makomar jam'iyyar dake da burin mulkar kasar na shekaru har 60 amma kuma ke nuna alamar kasawa tun kafin 20 din farko.