Zaman dar-dar lokacin mika takardun takara a Côte d'Ivoire
July 29, 2025
Sai dai, ana ci gaba da zaman dar dar a kasar sakamakon hana wasu manyan 'yan siyasa tsayawa takara da kotu ta yi, ciki har da tsohon shugaban kasa Laurent Gbagbo. Shugaban kasar Côte d'Ivoire Alassane Ouattara da ya dare kan kujerar mulki a shekara ta 2011, ya samu sahalewar jam'iyyarsa ta RHDP tun watan Juni wajen tsayawa takara karkashin inuwarta a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Oktoba mai zuwa.
Karin Bayani: Ouattara ya samu tabarrukin jam'iyyarsa wajen tsayawa takara
Sai dai a daya hannun kuwa, wasu 'yan adawa hudu na Côte d' Ivoire sun riga sun sa makomarsu, kasancewar an cire sunayensu daga cikin jerin sunayen masu kada kuri'a kamar yadda kotun kasar ta umurta, saboda ba su cancanci shiga wannan zaben ba. Na baya bayan nan ya kasance Tidjane Thiam, shugaban jam'iyyar PDCI, babbar jam'iyyar adawa, da tsohon shugaban kasa Laurent Gbagbo, da tsohon na hannun damansa Charles Blé Goudé, da kuma tsohon firayiminista kuma shugaban majalisar dokokin kasar, Guillaume Soro, wanda ke gudun hijira yanzu haka.
Amma Patrick Mboyo Bakambo, wani mai bincike a fannin shari'a da kimiyyar siyasa a Jami'ar Paris-Saclay a Faransa, kuma malami a Jami'ar Grenoble Alpes ya ce kawar da manyan abokan hamayyar siyasa ba sabon abu ba ne a Côte d'Ivoire.
Sai dai, uwargidar tsohon shugaban kasa Simone Gbagbo, za ta iya tsayawa takara a karkashin jam'iyyar MGC da ta kafa a watan Agustan shekarar 2022, bayan da aka yafe mata laifin da aka same ta da aikatawa. Shi ma tsohon firaminista Pascal Affi N'Guessan, wanda ke shugabantar jam'iyyar FPI ta Côte d' Ivoire da Laurent Gbagbo ya kafa na da damar tsayawa takara, saboda sunayensu na cikin kundin masu kada kuri'a.
Domin tsayawa takarar shugaban kasa a Côte d' Ivoire, dole ne dan takarar ya biya ajiya na CFA miliyan 50, kusan Euro 100,000. Sannan bisa ka'idar zabe, dole ne kowane dan takara ya samu sahalewar kashi 1% na masu kada kuri'a a cikin akalla kashi 50% na yankunan da kuma gundumomin Yamoussoukro da Abidjan. hasali ma dai, 'yan takara na da sauran wata guda don tattara amincewar 'yan kasa da ajiye takardun takara.
A lokacin zaben shugaban kasa na 2020, hudu daga cikin 'yan takara 44 ne kawai kotun tsarin mulki ta amince da takardunsu, yayin da ta ki amincewa da sauran 'yan takarar saboda rashin cika ka'ida.