1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Rashin tabbas kan rigakafin coronavirus a Najeriya

Muhammad Bello
December 22, 2020

Shirin gwamnatin Najeriya na sayo allurar rigakafin annobar coronavirus ya bar baya da kura inda 'yan majalisun tarayya na bayyana shakkun cewar gwamnatin ka iya alkinta wannan allura.

Südafrika Corona-Pandemie Soweto Test
Hoto: Jerome Delay/AP Photo/picture alliance

 

Ana dai cikin tirka tirka ne yanzu,na yadda gwamnatin ta Najeriya ta gabatar da bukatar sayo alluran na riga kafi na kimanin naira biliyan 400 ga Majalisar tarayar kasa,inda kuma ita majalisar ke kokwanton yadda Gwamnatin za ta iya alkinta alluran bayan auno su zuwa cikin kasar.Yan majalisar dai,na dubi ne ga yadda kafatanin asibitoci da kuma dakunan adana kayayyakin lafiya gami da kwararrun na harkokin lafiya ke karanci da kuma tabarbarewa a kasar.

Sai dai kuma, yayin da gwamnatin ta Najeriya ke bada tabbacin zaa iya alkinta wadannan allurai da kuma yin amfani da su ga yan kasa ba tare da mushkila ba,su kuma Yan Najeriyar na tunanin cewar  ne wadannan kudade da gwamnatin ke son samun sahalewar majalisun na kasa, ka iya karkewa a aljifan wasu kusoshin na gwamnati da ke da halayyar bera.

Majalisar Dattawa ta kasar dai, ta ce sayo wannan allura ta riga kafin annobar ta corona na da mahimmanci kwarai, tun da dai kariya ce za a bai wa 'yan Najeriya, to amma dai, majalisar ta kafe cewar tana jira ta ga yadda bangaren gwamnati mai zartarwa zai nunar da shirin da ke kasa na iya alkinta wannan kaya na kariya ga jama'a.

Cibiyar dakile bazuwar cututtuka dai ta kasa, NCDC, tuni ta fara bayyana alkaluman masu kamuwa da kuma mutuwa a sakamakon wannan annoba da yanzu ke cikin zango na biyu, mai nunin cewar lallai lamarin na annobar ta coronavirus na dada kazanta a kasar, inda ta kai sabbin kamu sun kai mutane 356.