Rudani tsakanin Najeriya da Libya kan Super Eagles
October 15, 2024Wannan takadama a kan wasan kwallon kafa ta fara zafi sosai inda Libyan ta yi barazanar kai Najeriya kara yayin da ita kuma Najeriya ke cewa an ci zarafin 'yan wasan ta. Maimakon wasan kwallon kafa ya zama hanya ta kula kawance a tsakanin kasashe. Kungiyar kwallon kafan Najeriya Super Eagles ta je kasar Libya domin buga wasan da zai karafafa zuwamunci amma sai ya zama akasin haka, domin ya kasance cike da zargi na cin mutunci da rashin girmama bako.
Duk da cewa 'yan wasan na Najeriya sun koma gida cikin koshin lafiya amma a bayyane ta ke cewa lamarin ya bata wa mahukuntan Najeriya da na hukumar kwallon kafar kasar domin ta kai ga shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu sanya baki ta hannun ma'aikatar kula da harkokin kasashen waje kafin ceto ‘yan wasan na Najeriya daga filin jiragen sama na Albaraq na Libya inda aka karkatar da jirgin maimakon su sauka a Benghazi.
Kungiyar kula da kwallon kafa ta Afrika ta ce Lamari irin wannan da ya hada kasa da kasa na taba dangantaka ta diplomasiyya abin da ya sanya kai ga sanya bakin mahukuntan kasashen biyu. Tuni mahukuntan kasar Libya suka yi kurarin kai Najeriya kara a gaban hukumar kula da kwallon kafa ta kasashen Afrika a kan cewa sun barsu cikin shirin buga kwallo amma jiran ya zaman a gawon shannu.
A halin da ake ciki dai hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar Afrika ta kadammar da bincike a kan abin da ya faru bayan da kasar Libya ta yi barazanar kai Najeriya kara a kan abin da ta yi zargi da makarkashiya ce Najeriyar ke yi mata.