1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici ya mamaye cikin gidan jam'iyyar PDP ta 'yan hamayya

Uwais Abubakar Idris AMA
October 14, 2024

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya na cikin wadi na tsaka mai wuya sakamakon rikicin cikin gida mai tsanani da take fuskanta.

Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben 2023 Alhaji Atiku Abubakar
Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben 2023 Alhaji Atiku AbubakarHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

Rikicin manyan bangarori guda biyu na jamiyyar PDP mai adawa na kara kamari, bangarorin da ke ja-in-ja kan batun wanda zai jagorancin jamiyyar tun bayan sauke shugabanta Iyorchia Ayu da ya fito daga yankin Arewa maso tsakiyar Najeriya. Tun bayan da aka bai wa  Ambassada Iliya Damagum shugabancin jam'iyyar hakan ya haifar da rarabuwar kawuna daga kwamitin zartaswa har zuwa ga na amintatun jamiyyar

Karin bayani: Jam'iyyar PdP ta Najeriya na cikin rudani

Wakilan jam'iyyar PDP mai adawa a NajeriyaHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Sabon shugaban riko Ahmed Yayari ya bayyana cewa ya amincewa da mukamin shugabancin PDP da ka nada shi na riko, tare da cewa ba zai bata lokaci ba wajen yi wa jamiyyar sauye-sauye, har ma ya bukaci sashen Arewa maso tsakiyar Najeriya ya fitar da mutumin da zai karbi jagoranci kamar yadda PDP ta tsara.

Karin bayani: Sabon rikicin siyasa a Rivers ta Najeriya

Gwamnan Bauchi Bala Mohammed kusa a jam'iyyar PDPHoto: Ubale Musa/DW

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed, ya yi kokarin warware barakar da ta kunno kai a cikin gidan jam'iyyar, sai dai hakan yaci tura, domin a yanzu ta tabbata da cewa PDP na da shugabani biyu dukkaninsu na riko, kana ana sa ran gwamnonin jamiyyar su gudanar da taro domin kokarin rarrabe aya da tsakuwa kan wannan rikicin da ke kara tayar da kura a babbar jam'iyyar 'yan adawa ta Najeriya.